Zico zai horar da FC Goa ta India

Zico Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Tsohon dan kwallon Brazil ya koma koci a Indiya

Tsohon shahararren dan kwallon Brazil Zico, zai horas da kungiyar FC Goa wadda take buga gasar cin kofin Indiya wato Super League.

Mai shekaru 61 da haihuwa, ya buga wa Brazil wasanni 71, ciki har da gasar cin kofin duniya a shekarar 1978 da 1982 da 1986.

Haka kuma ya horas da tamaula a Brazil da Japan da Turkiya da Girka da iran da kuma Qatar.

A wani jawabin da kungiyar ta sanar ta ce "Ziko ya rattaba kwantiragi da mu a Rio de Janeiro da ke Brazil.

Hukumar kwallon kafar Indiya na kokarin ganin ta bunkasa wasan tamaula a kasar, inda za a fara kakar bana a watan Oktoba.