'Kamaru za ta dawo da tagomashinta'

Cameroon Team Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin yana fatan dawo da tagomashin kasar a tamaula

Kocin Kamaru Volker Finke ya ce yana kokarin dawo da tagomashin kasar, bayan da ta kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.

Kamaru ta gamu da boren tawagar 'yan kwallonta saboda rashin biyan ladan wasa, sannan ta yi rashin nasarar wasanni uku da ta buga a kofin duniya.

Haka kuma 'yan wasanta biyu sun yi fada a fili lokacin gasar, an kuma bai wa Alex Song jan kati aka kuma dakatar da shi buga wasanni uku.

An kuma zargi kasar da cogen wasa, wanda Kamaru ta kafa kwamitin bincike kan zargin wanda har yanzu ba a fitar da sakamakon sa ba.

Kamaru za ta kara da Jamhuriyar Congo a Lubumbashi kafin ta karbi bakuncin Ivory Coast a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka.