Ingila ta doke Norway da ci 1-0

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rooney ya zura kwallo a matsayinsa na kyaftin din Ingila

Kasar Ingila ta doke Norway da ci daya mai ban haushi, a wasan sada zumunci da suka kara a filin Wembley ranar Laraba.

'Yan kallo 40,181 ne suka kalli fafatarwar wanda ya kasance wasa mafi karancin 'yan kallo da suka kalli wasan Ingila a Wembley.

Rooney ne ya zura kwallo tilo a ragar Norway a minti na 68, a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da Omar Elabdellaoui ya yi wa Raheem Sterling keta a da'ira ta 18.

Ingila za ta kara da Switzerland ranar Litinin a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai ranar Litinin.

Ga sakamakon sauran wasanin sada zumunci da aka buga

Germany 2 - 4 Argentina Jamhuriyar Ireland 2 - 0 Oman Russia 4 - 0 Azerbaijan Lithuania 1 - 1 Hadaddiyar Daular Larabawa Ukraine 1 - 0 Moldova Latvia 2 - 0 Armenia Denmark 1 - 2 Turkey Jamhuriyar Czech 0 - 1 Amurka