Ba Ozil a karawa da Argentina

Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus na sa ran Ozil zai buga mata wasa ranar Lahadi

Dan kwallon Jamus Mesut Ozil, ba zai buga wasan sada zumunci da kasar za ta buga da Argentina ranar Laraba ba.

Dan kwallon mai shekaru 25 ya ji rauni daf a tashi wasan da suka tashi kunnen doki da Leicester ranar Lahadi data gabata.

Jamus za ta buga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da Scotland ranar Lahadi.

Manajan tawagar 'yan kwallon Jamus Oliver Bierhoff ya ce "Muna bukatar dan wasan ya buga mana kwallo, amma muna sa ran zai iya wasa ranar Lahadi".