Waris: Na koma Turkiya tamaula da buri

Majeed Waris Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yana fatan zai taka rawar gani a kulob din

Dan kwallon Ghana Majeed Waris ya ce ya koma kulob din Trabzonspor na Turkiya domin kyawawan burin da kungiyar take da shi.

Waris, mai shekaru 22, ya koma kungiyar ne daga Sparttak Moscow ta Rasha ranar Litinin, bayan da ya ki amincewa da zawarcin wasu kungiyoyin Turai.

Dan kwallon ya ce "Na gamsu da 'yan wasan da kulob din yake da shi, da tsarin shirye-shiryensa, ga shi yana buga gasar zakarun Turai".

Waris ya kwashe rabin kakar bara a kungiyar Valenciennes ta Faransa, inda ya buga mata wasa aro ya kuma zura kwallaye tara a wasanni 16.

Black Stars ta Ghana za ta karbi bakuncin Uganda a Kumasi ranar Asabar kafin ta fafata da Togo kwanaki biyar tsakani a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka.