Rojo ya samu izinin wasa a Ingila

Marcos Rojo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rojo zai buga karawa da QPR da United za tayi a Premier

Sabon dan kwallon Manchester United Marcos Rojo wanda ta dauko kan kudi fam miliyan 16, ya samu takardun izinin buga tamaula a Ingila.

Dan wasan Argentina mai shekaru 24, ya koma United ne daga Sporting Lisbon kwanaki 16 baya, amma har yanzu bai buga wa kungiyar kwallo ba.

An ce ya gamu da tsaikon ne domin shari'ar da zai fuskanta tsakaninsa da makwabcinsa a Argentina da suka samu sabani a shekarar 2010.

United ta rubuta a shafinta na Twitter cewa Rojo ya samu dukkan takardun da suka kamata kuma a shirye yake ya fara wasa da United za ta kara da QPR ranar 14 ga watan Satumba.

Tun lokacin da United ta dauko dan kwallon bai buga karawar da kungiyar ta yi da Sunderland da kuma wasan da MK Dons ta doke United a Capital One da kuma wasa da Burnley.