Giwa ba zai bar kujerar NFF ba duk da..

NFF Logo
Image caption Nigeria za ta kara da Congo ranar Asabar a Calaba

Chris Giwa ya nace ba zai bar kujerar shugabancin hukumar kwallon kafar Nigeria NFF ba duk da wa'adin da FIFA ta bashi da ya sauka nan da ranar Litinin.

Fifa ta bai wa NFF sharadin dawo da Aminu Maigari da kuma shirya ranar sabon zaben hukumar ko kuma ta fuskanci hukunci da zai hada da dakatar da ita shiga harkar kwallon kafa.

Giwa ya sanar wa da BBC cewa "zan ci gaba da zama a matsayin sabon shugaban hukumar NFF tun da zabe na aka yi bisa kan doka".

"Na fada a baya cewa duk wanda yake da korafi, ya kamata ya rubutawa kwamitin daukaka kara na hukumar kwallon kafar NFF".

"Idan har kwamitin daukaka karar wasanni ya zauna kan korafin zabe na ya kuma ce na sauka daga kan kujera, to zan yi biyayya".

Idan har Giwa ya nace ya ki barin ofis kuma FIFA ta dakatar da Nigeriya daga shiga wasan kwallon kafa, to ba za ta kara da Afirka ta kudu a wasan neman tikitin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka ranar Laraba ba.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta ce idan har Nigeria ba ta buga karawa da Afirka ta Kudu ranar Laraba ba, to za ta kore ta daga wasannin neman gurbin cin gasar kofin Nahiyar Afirka.

Fifa za ta janye takunkumi ne idan NFF ta mayar da Aminu Maigari kan kujerarsa, sannan ya tsara ranar da za a gudanar da sabon zabe.

An taba dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa a watan Yuli, lokacin da gwamnati ta tsoma baki a harkar kwallon kafa.