Odemwinge zai yi jinyar rauni

Peter Odemwingie Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Dan wasan zai yi jinya har zuwa watan Janairun badi

Dan kwallon Nigeria mai wasa a kulob din Stoke City Peter Odemwingie zai yi jinyar rauni da ya ji a gwiwarsa na tsawon lokaci mai tsawo.

Odemwingie ya ji raunin ne a karawar da suka yi da Manchester City a gasar Premier wasan mako na uku, wanda suka lashe wasa da ci 1-0 ranar Asabar.

Kocin Stoke Mark Hughes ya ce "Raunin mai wuyar sha'ani ne kuma abin takaici, domin zai dauki tsawon lokaci yana jinya".

A bara kulob din Stoke ya lashe wasanni bakwai cikin 15 da Odemwingie ya buga wasa, idan aka auna doke wasa tara cikin 29 da bai buga wasa ba tun lokacin da ya koma kungiyar a watan Janairu.

Stoke City ta cire sunan Odemwingie daga cikin 'yan wasanta 25 da za su fafata a gasar Premier, hakan na nufin zai yi jinyar rauni har zuwa watan Janairun badi.