Raunin dan wasa zai ja wa Newcastle

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sai dai Pardew ya yi amfani da Ayoze Perez ko Facundo Ferreyra, da kuma Remy Cabella

Dan wasan Newcastle Siem de Jong ka iya shafe tsawon watanni bai taka leda ba, saboda raunin da ya ji a cinya.

Dan wasan na kasar Holland mai shekara 25,ya shiga Newcastle United daga Ajax a watan Yuli, haka kuma za a tantance tsananin raunin da ya ji a cinyarsa yayin atisaye a makon gobe.

Wani mai magana yawun kulob din ya ce "alamun farko sun nuna cewa mai yiwuwa ne sai ya yi jinyar watanni."

De Jong ya yi wasanni uku a wannan kaka da Newcastle, ko da yake har yanzu kungiyar ba ta ci wasa a gasar ta Firmiya ba.

Jinyar De Jong ta bar kocin Newcastle Alan Pardew da rashin zabin 'yan wasansa na gaba, yayin da dan wasan tsakiya na kulob din Hatem Ben Arfa ya koma kungiyar Hull kafin rufe lokacin musayar 'yan wasa.