CAF U-17: An kori Benin daga wasa

Caf Logo Hakkin mallakar hoto
Image caption Sau biyu kenan CAF na hukunci kan amfani da 'yan kwallon da suka haura ka'ida

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Afirka CAF ta kori kasar Benin daga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin matasa 'yan kasa da Shekaru 17 ta Afirka.

CAF ta yanke hukuncin ne saboda samun Benin da laifin amfani da 'yan kwallo hudu da shekarunsu suka haura ka'ida a karawar da su kayi da Mali.

Hakan na nufin Mali ta samu damar buga wasan gaba, inda za ta kara da Tunisia a wasan karshe na samun tikitin shiga gasar.

Haka kuma bayan korar da aka yiwa Benin, an kuma dakatar da kasar shiga wasannin matasa 'yan kasa da shekaru 17 da 20 da 23 har tsawon shekaru biyu.

Wannan shi ne karo na biyu da CAF ta hukunta kasashen da su kayi amfani da 'yan kwallon da shekarunsu ya haura doka, tun lokacin da aka samu Gambia da laifi a wasan matasa 'yan kasa da shekaru 20 a watan Afirilu.

Hukuncin da a ka yiwa Gambia ya kunshi hana ta shiga harkar kwallon kafa a Afirka, saboda samunta da aikata laifi da gangan.