FIFA na zargin jami'inta kan cin hanci

Canover Watson Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hukumar FIFA za ta ci gaba da bibiyar ba'asi ranar 28 ga watan Satumba

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA tana zargin jami'inta Canover Watson da cin hanshi da rashawa da almundahana da kudade a tsibirin Cayman.

Tuni hukumar ta sa aka tsare jami'in domin ya bada ba'asi kan zargin da ake masa na yin ruf da ciki da rufa rufa.

Canover Watson daya ne daga cikin mambobin hukumar FIFA tara da ke bincike kudi kuma shi ne mataimakin shugaban kwallon kafa na yankin Caribbean.

Sai dai Watson ya musanta zargin wanda tuni aka bada shi beli, da zummar zai kai kanshi wajen jami'an tsaro ranar 28 ga watan Satumba.

Sashin binciken kudi na FIFA shi ne yake da alhaki tare da tabbatar da bin ka'ida wajen tara kudade da kuma kashe su.