Euro 2016: Jamus da Scotland

Darren Fletcher Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Fletcher ya ce za su buga kwallo da nufin samun maki a Jamus

Kasar Jamus mai rike da kofin duniya za ta karbi bakuncin Scotland a wasan neman tikitin shiga gasar wasan cin kofin Nahiyar Turai.

Kyaftin din Scotland Darren Fletcher ya ce a shirye su ke da fuskantar kalu balen dake gabansu musammam karawa da mai kofin duniya kuma a gidansu.

Wannan shi ne karo na farko da kyaftin din zai buga wa kasar wasa tun lokacin da ya yi jinyar rauni na tsawon lokaci.

Jamus ta yi rashin Nasara a hannun Argentina har gida da ci 4-2 a wasan sada zumunci da su ka kara ranar Laraba.

Fletcher ya ce Jamus tana fama da 'yan wasanta da su ke jinyar rauni, sannan ga Miroslav Klose da Per Mertesacker da kuma Philipp Lahm da su kayi ritayar buga mata tamaula.

Ga sauran wasannin da za a kara:

Georgia v R. of Ireland

Germany v Scotland

Hungary v Northern Ireland

Gibraltar v Poland

Faroe Islands v Finland

Greece v Romania

Denmark v Armenia

Portugal v Albania