UEFA ta hukunta Steaua da Ludogorets

Steaua Bucharest Ludogorets Hakkin mallakar hoto epa
Image caption UEFA ta ce bata amince da tashin hankali da kalamun wariya ba a kwallo

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA ta hukunta kulob din Steaua Bucharest na Romania da buga wasanni biyu babu 'yan kallo.

Itama kungiyar Ludogorets Razgrad za ta rufe wani sashi a filin wasanta lokacin da za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar kofin zakarun Turai ranar 1 ga watan Satumba.

UEFA ta samu kungiyoyin biyu ne da laifin kalamun wariya lokacin da Ludogorets ta karbi bakuncin Steaua a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Hukuncin Steaua zai fara aiki ne lokacin da za su kara da Aalborg ranar 18 ga watan Satumba.

UEFA ta kuma ci tarar Bucharest fan 40,000 saboda kalamun wariya daga magoya bayanta da fan 8,000 da 'yan kallo suka kunna hayaki da jifa cikin fili da kuma karin fan 3,600 saboda karbar katin gargadi guda biyar da 'yan wasa suka samu a karawar.

Ludogorets za ta biya fam 4,750 saboda 'yan wasanta sama da biyar sun karbi katin gargadi da kuma fan 4,000 da magoya bayanta suka shiga fili.