Brazil ta ajiye Maicon daga tawagar ta

Maicon Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan tagomashinsa ya kare, inda ya kasa taka rawar gani a City

Kasar Brazil ta ajiye dan kwallonta mai tsaron baya Maicon daga shiga cikin tawagar 'yan wasan kasar, saboda samunsa da laifin aikata rashin da'a.

Brazil wadda ta lashe kofin duniya karo biyar, za ta kara da Ecuador a wasan sada zumunci da za su fafata a New York ranar Talata.

Sai dai Maicon mai buga tamaula a Roma mai shekaru 33, wanda ya buga wa Brazil wasanni 76, ba zai samu damar buga wasa ba a karkashin sabon koci Dunga.

Maicon ya buga karawar da Brazil ta lashe Colombia da ci 1-0 karkashin jagorancin koci Dunga a wasan farko da ya jagoranci kasar ranar Asabar.

Ya koma Manchester City daga Inter Milan a watan Agustan 2012 kan kudi fam miliyan uku, amma ya kasa tabuka rawar gani a gasar Premier.

Ya kuma kammala koma wa kasar Italiya wasa da kulob din Roma a watan Yulin 2013, bayan da ya buga wasanni tara a Manchester City.