Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0

Danny Welbeck Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ta fara wasan neman shiga gasar kofin Turai da kafar dama

Ingila ta doke Switzerland har gida da ci 2-0 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da su ka kara a filin St Jakob-Park ranar Litinin.

Dan kwallon da Arsenal ta sayo daga Manchester United Danny Welbeck ne ya zura kwallaye biyu a raga a minti na 58 da kuma 90.

Ingila tana rukuni na biyar da ya kunshi Lithuania da Estonia da Slovenia da San Marino da kuma Switzerland.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Luxembourg 1 - 1 Belarus Spain 5 - 1 Macedonia Ukraine 0 - 1 Slovakia Estonia 1 - 0 Slovenia San Marino 0 - 2 Lithuania Russia 4 - 0 Liechtenstein Austria 1 - 1 Sweden Montenegro 2 - 0 Moldova