Zan koma kujera ta - Maigari

Aminu Maigari Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Shugaban ya ce zai koma kan kujerarsa da kuma shirya ranar zabe

Shugaban hukumar kwallon kafa na Nigeria (NFF) Aminu Maigari ya ce zai koma kujerarsa don ci gaba da gudanar da aiki kamar yadda FIFA ta umarta ranar Talata.

Maigari ya sanar wa da BBC ta wayar salulu ce wa "Zan koma ofis a ranar Talata, domin ci gaba da gudanar da aiki da kuma tsara ranar da za'a gudanar da sabon zabe".

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ce ta baiwa Chris Giwa wa'adin ya bar kujerar NFF ranar Litinin ko kuma Nigeria ta fuskanci hukunci.

Jami'in yada labarai na hukumar NFF Ademola Olajire ya tabbatar da cewa Chris Giwa bai shiga hedikwatar hukumar ba ranar Litinin.

Sai dai sakatare janar na hukumar Musa Ahmadu da sauran daraktoci sun shiga shalkwatar hukumar wanda rabonsu da shiga tun ranar 26 ga watan Agusta.

FIFA ta ki amincewa da zaben Chris Giwa wanda ya dare kujerar NFF tun ranar 26 ga watan Agusta a lokacin babban taron hukumar, wanda ya zo da takaddama bayan da jami'an tsaro suka gayyaci Aminu Maigari ofishinsu domin amsa tambayoyi.

Sau biyu hukumar kwallon kafa ta Najeria tana maida Aminu Maigari kan kujerarsa, bayan da wata kotu a Jos ta dakatar da shi da kuma kwamitin amintattun NFF da ya sauke shi daga kan kujerarsa.

Ko a watan Yuli FIFA ta dakatar da Nigeria daga shiga harkar wasan kwallon kafa, wanda aka dauki kwanaki tara kafin a gano bakin zaren.