An dakatar da dan kwallo buga wasanni 70

Referee Ban Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce bada gangan ya doki alkalin wasan ba

An hukunta dan wasan Australia Ismail Gunduz cewa ba zai buga wasanni 70 ba, saboda samunsa da laifin yi wa alkalin wasa karo da kansa.

Gunduz mai kwallo a kulob din SK Rum ya tashi hankalinsa lokacin da alkalin wasa ya bashi katin gargadi na biyu a minti na 78 a karawar da suka yi da SPG Innsbruck West.

Tuni kocin SK Rum Michael Messner ya nisanta kansa da halayyar dan wasan, harma ya ce sun raba gari da shi.

Bayan da aka dakatar da dan wasan buga wasanni 70, sannan an ci kulob dinsa tarar fam 204.

Sai dai dan kwallon ya yi mamakin hukuncin da aka yanke masa, sannan ya ce zamewa ya yi a filin inda ya doke alkalin wasa lokacin da zai fadi kasa.