US Open: Nishikori da Cilic a wasan karshe

Marin Cilic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da a kara a wasan karshe babu manyan 'yan wasa tun shekarar 2005

Kei Nishikori da Marin Cilic za su kara a wasan karshe na cin kofin US Open a gasar wasan kwallon tennis ranar Litinin.

Ranar Asabar ne Nishikori na kasar Japan ya yi waje da Novak Djokovic na Serbia daga gasar, yayinda Cilic na Crotia ya doke Roger Federer na Switzerland.

Wannan shi ne karawar wasan karshe da za'a yi babu manyan 'yan kwallon tennis tsakanin Djokovic da Federer ko kuma Rafael Nadal tun daga shekarar 2005.

An yi hasashen cewa Nishikori ne zai lashe wasan, sai dai Cilic ba kanwar lasa bane a wasan kwallon Tennis.