'Karawa da Afirka ta Kudu sai an tashi'

Stephen Keshi
Image caption Keshi ya ce za su sa kaimi domin su doke Bafana Bafana

Kocin Super Eagles Stephen Keshi ya ce karawar da za su yi da Afirka ta Kudu a wasan neman tikitin shiga kofin Nahiyar Afirka tamkar wasan cin kofin duniya za su buga wasan.

Keshi ya ce wasan yana da muhimmanci matuka ga Nigeria, kuma karawar za ta haskaka musu hanyar samun tikitin zuwa Morocco a badi domin kare kambu.

Super Eagles ta sha kashi a hannun Congo Brazaville da ci 3-2 ranar Asabar, wanda shi ne karon farko da Nigeria ta yi rashin nasara a Calaba.

Kasar Afirka ta Kudu ta doke Sudan har gida da ci 3-0, inda kasar ta kara samunkwarin gwiwar za su iya lashe Nigeria a fafatawar da za suyi ranar Laraba.

Golan Super Eagles Austin Ejide ya ce za su zage damtse a karawar da nufin lashe wasan, duk da cewa yanzu kowa ya iya taka leda a duniya.