Karon battar tamaular Afirka ran Laraba

CAF Logo
Image caption Wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Afirka 2015

Kasar Afirka ta Kudu na fatan doke Nigeria a karawar da za su yi a wasan neman tikitin shiga gasar kofin nahiyar Afirka ranar Laraba.

Nigeria mai rike da kofin Nahiyar Afirka ta doke Afirka ta Kudu a wasanni biyar da kunnen doki a wasa daya daga cikin wasanni shida da suka fafata a shekarar 2014.

Bafana Bafana ta kasa doke Super Eagles a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da kuma na nahiyar Afirka, sannan ta kasa zura kwallo a ragar Nigeria.

Kamaru za ta karbi bakuncin Ivory Coast a wasan rukuni na hudu, ranar Asabar data gabata, kuma Kamaru ce ta doke Congo har gida da ci 2-0, inda Ivory Coast ta lashe Saliyo da ci 2-1.

Ghana za ta ziyarci Togo a fafatawar da za su yi a filin wasa na Stade de Kegue, bayan da Ghana ta tashi wasa 1-1 a karawar da tayi da Uganda ranar Asabar.

Sauran wasannin da za a barje gumi sun hada da kai ruwa rana tsakanin Algeria da Mali, sai kuma Masar da za ta karbi bakuncin Tunisia a wasan hamayya.

Ga ragowar wasannin da za a kara:

Malawi vs Ethiopia Sierra Leone vs Congo, Congo vs Sudan Mozambique vs Niger Cape Verde vs Zambia Angola vs Burkina Faso Uganda vs Guinea Lesotho vs Gabon Botswana vs Senegal