Dokar raunin dan kwallo a ka za ta fara aiki

Head Injury Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption FIFA za ta kaddamar da dokar da za a duba dan kwallo idan ya ji rauni a kansa

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta fara amfani da sabuwar dokar jin raunin dan kwallo a kansa da yadda ya kamata a duba lafiyarsa a watan Oktoba.

Shugaban kwamitin lafiya na hukumar FIFA Michel D'Hooghe ya bada shawarar tsayar da tamaula na tsawon minti uku lokacin da ake duba da lafiyar dan kwallo da ya gamu da rauni ko bugu a kansa.

Kuma likitan kulob ne zai yanke shawarar ko dan wasa zai iya ci gaba da buga kwallo ko kuma a sauya shi ba kociya ba.

D'Hooghe zai gabatar da shawarwarinsa a taron hukumar kwallon Turai UEFA na ranar 18 ga watan Satumba da kuma a gaban FIFA mako guda tsakani.

Dokar dai irin wadda aka kafa ne a gasar cin kofin Premier a farkon kakar wasan bana.

Idan har FIFA da UEFA suka amince da dokar, to za a fara gudanar da ita a watan Oktoba, sannan a yi amfani da ita a gasar kofin zakarun Turai da sauran manyan wasanni.

A bara an soki kulob din Tottenham da barin gola Hugo Lloris ya koma wasa, bayan da ya fita daga hayyacinsa a karawar da suka tashi canjaras da Everton.