Man United za ta dawo da tagomashinta

Di Maria Woodward Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Woodward ya ce United na daukar matakan da ya dace don ganin ta sake yin fice

Mataimakin shugaban kulob din Manchester United Ed Woodward ya ce kungiyar na daf da dawo da tagomashinta.

Woodward ya fadi hakan ne a lokacin taron masu hannun jarin kungiyar da ta sanar da samun karin kudin shiga da ya kai kaso 19 cikin dari kimanin sama da fam miliyan 433, amma ta samu faduwa da ta kai kaso 84 cikin dari.

Mataimakin shugaban ya ce "Shekarar 2013 zuwa 14 kungiyar ta yi fama da kalu-bale da takaicin yadda ta kammala kakar wasan badi".

"Muna da tabbacin dauko koci da ya yi fice a duniya zai sauya halin da muka shiga, saboda haka nan ba da dadewa ba za mu dawo da tagomashinmu".

Woodward ya ce sun samu karin kudin shiga kaso sama da 24 bisa cikin dari da ya kai sama da fam miliyan 189, bayan kulla yarje-jeniya da kamfanin Adidas.