Platini ya zargi FIFA kan bambanci

Michel Platini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Platini ya dade yana kalubalantar hukumar FIFA

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini, ya zargi hukumar kwallon kafa na duniya FIFA da nuna bambanci a gasar cin kofin duniya.

Platinin ya ce yana da kyau a kafa kwamitin sa ido, sai dai ba za su iya gudanar da aikinsu ba idan babu doka da oda da kuma kayan aiki.

Ya kara da cewa hukumar kwallon kafar Turai tana sa ido sosai a manyan wasanni domin kaucewa fadawa rikici a wasa, amma a gasar kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci babu wani tanadi da FIFA ta yi.

Ana danganta kalaman Platini da halin da magoya bayan kasar Mexico suka nuna na cin zarafin mai tsaron raga da kalamun wariya a gasar cin kofin duniya da aka kammala a bana.

Shugaban kwamitin ladabtar wa na hukumar FIFA Claudio Sulser ya ce kalaman da magoya bayan Mexico suka dinga yi a lokacin gasar kofin duniya ba suyi shi kai tsaye ga dan wasa ba.

FIFA bata dauki mataki ba akan magoya bayan Jamus lokacin da suka shafe fuskarsu da bakin fenti, da kuma magoya bayan Croatia da suka dinga daga tutar 'yan Nazi.

Platini ya ce kwallon kafa madubin al'umma ce da take haskaka al'adu ta kuma sada zumunci tsakanin al'umma.