Afirka ta Kudu za ta karbi bakucin Nigeria

Nigeria Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption South Afirka na fatan lashe Nigeria a wannan karon

Kasar Afirka ta kudu za ta karbi bakuncin Nigeria a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a badi.

Nigeria mai rike da kofin Afirka tayi rashin nasara a hannun Congo Brazaville da ci 3-2 har gida, inda Afirka ta kudu ta doke Sudan har gida da ci 3-0 ranar Asabar.

Kocin Nigeria Stephen Keshi ya ce za su buga wasan ne tamkar cin kofin duniya, shi kuwa Ephraim Shakes Mashaba kocin Afirka ta Kudu ya ce za su kawo karshen doke su da Nigeria ke yi a duk haduwa.

Kimanin wasanni 14 za'a kara domin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a filaye daban-daban ranar Laraba.

Rukunin A Congo v Sudan South Africa v Nigeria Rukunin B Malawi v Ethiopia Algeria v Mali Rukunin C Angola v Burkina Faso Lesotho v Gabon Rukunin D Cameroon v Ivory Coast Sierra Leone v DR Congo Rukunin E Togo v Ghana Uganda v Guinea Rukunin F Mozambique v Niger Cape Verde v Zambia Rukunin G Botswana v Senegal Egypt v Tunisia