Agbonlahor ya tsawaita kwantiraginsa da Villa

Gebriel Agbonlahor Hakkin mallakar hoto avfofficial
Image caption Agbonlahor dan kwallon Ingila da ya buga mata wasanni uku

Dan wasan Aston Villa mai zura kwallo a raga Gabriel Agbonlahor ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din na tsawon shekaru hudu.

Dan kwallon mai shekaru 27 ya dauki tsawon lokaci yana buga tamaula a Villa Park, kuma Villa ta taba ba da shi aro ga Sheffield Wednesday da Watford.

Agbonlahor ya buga wa Villa wasanni 276 inda ya zura kwallaye 60 a raga, ya kuma buga wa Ingila tamaula karo uku, a wasan karshe da ya buga mata shi ne a shekarar 2009.

Dan wasan ya ce "Kwanci tashi ba wuya, har na kwashe shekaru goma a Villa, kuma ina tuna ranar da na fara buga mata wasan farko".

Ya kara da cewa yana cike da murnar sake rattaba hannu a kwantiragin shekaru hudu da kulob din da zai bashi damar kara bada gudunmawarsa.