Rafalin kwallon Nigeria za su koma busa Laraba

Referees Whistle
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na 26 ranar Laraba

Shugaban kungiyar alkalan wasan kwallon kafa na Nigeria Ahmed Maude ya ce sun janye yajin aikin da suka yi kan busa wasannin Premier kasar.

Maude ya sanar wa da BBC cewa sun kawo karshen yajin aikin ne bayan da aka kawo karshen takaddamar dake hukumar kwallon kafar Nigeria NFF.

Ya kuma kara da cewa sun shiga yajin aikin ne domin nema wa Nigeria mafita ganin yadda ake kokarin maida hannun agogo baya a harkar kwallon kafar kasar.

Alkalan wasan kwallon kafar Nigeria sun shiga yajin aiki ne tun lokacin da taron hukumar NFF ya zo da tangarda, har aka ce an zabi Chriss Giwa a matsayin sabon shugaban hukumar.

Za a dawo da wasannin cin kofin Premier ne a karawar mako na 26 ranar Laraba 17 ga watan Satumba.

Gasar wasan cin kofin Premier Nigeria ya gamu da koma baya sau tari, ganin gasar bana ma da ake buga wa ta shekarar 2013-14 ce.