Kocin kwallon mata na Nigeria Effiom ya mutu

Ntiero Effiom Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon kocin Super Falcons ta Nigeria wanda ya mutu

Tsohon kocin tawagar kwallon kafar mata na Nigeria Ntiero Effiom wanda ya ya jagoranci kasar ta lashe kofin Afirka karo biyar a shekarar 2006 ya mutu a jihar Cross River, bayan fama da rashin lafiya.

Effiom ya kuma horas da Super Falcons a gasar kofin duniya a shekarar 2007 da China ta karbi bakunci, ya kuma mutu ne ranar Talata bayan gamu wa da shanyewar barin jiki kamar yadda matarsa ta bayyana.

Cynthia Uwak 'yan wasan da ta yi fice a Afirka karo biyu ta bayyana shi da cewa "Mutum ne na kirki da za'a iya kowar halayyarsa, ko yaushe yana bani amannar zan iya taka rawa a wasa".

"Har yanzu ina cikin jimami wanda na kasa cewa komai, illa kawai na yi masa addu'a".

Effiom ya yi kocin kulob din Pelican Stars ta jihar Cross River, inda ya lashe kofunan Premier Nigeria da dama kafin a nada shi kocin mata na matasa 'yan kasa da shekaru 19 da su ka wakilci kasar a gasar kofin duniya a shekarar 2002 a Canada.

Shekaru biyu kuma aka nada shi mai horas da Super Falcons. Effiom ya yi ritaya daga aikin gwamnati a watan Satumbar 2013.