Amurka ta dauki kofin Duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun farkon wasan Amurka ta mamaye Serbia

Amurka ta dauki kofin gasar duniya na kwallon kwando a karo na biyar bayan ta doke Serbia da ci 129 da 92 a Madrid.

'Yan wasan na Amurka da daman ake ganin za su sake daukar kofin sun mamaye wasan da takwarorin nasu na Serbia suka kasa katabus tun farkon wasan.

Dan wasan Cleveland Kyrie Irving shi ne kan gaba wajen ci wa Amurka kwallon, inda ya jefa 26 a kwando.

Shi kuma James Harden na Houston ya jefa 23.

Nikola Kalinic da Nemanja Bjelica kowannensu ya ci wa Serbia kwallaye 18.