Louis van Gaal na harin Premier

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption ''Ina son in bai wa magoya bayan Man United kofi.''

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce, burinsa shi ne ya dawo da kofin Premier Old Trafford.

Nasarar ci 4-0 akan QPR ita ce ta Premier ta farko da Man U ta samu tun lokacin da sabon kocin ya kama aiki a bana.

Wannan kokari da Manchestern ta yi a gida shi ne ya sa kocin ya furta hakan.

Van Gaal ya ce, ''ina son daukar Premier, idan ba bana ba to a shekara mai zuwa ko kuma shekara ta uku.''

Shugaban kungiyar ta Man United Ed Woodward ya gindaya wa kocin dan kasar Holland sharadin kai kungiyar akalla matsayi na uku a Premiern.

Wasan da United din ta yi da QPR wanda shi ne na hudu a Premier, da ta sa Angel di Maria da Ander Herrera ya nuna alamun farfadowarta.

Angel di Maria ne ya fara ci mata kwallo a wasan a minti na 24, sai Herrera a minti na 36 sai Rooney a minti na 44 sai kuma Mata a minti na 58.

Shi dai van Gaal ya dauki kofin La Liga na Spain a shekararsa ta farko da Barcelona da kuma na Bundesliga na Jamus shi ma a skekararsa ta farko da Bayern Munich.

Wasan Premier daya kawai za a yi ranar Litinin din nan, tsakanin Hull City da West Ham.

Karin bayani