Firimiyar bana ta Man United ce-Van Gaal

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ya ce a matsayinka na koci idan kungiyarka ta ci 4-0, dole ne ka yi farin ciki amma duk da haka akwai inda za a yi gyara

Kocin Manchester United Louis Van Gaal ya ce burinsa kawai shi ne ya ciyo wa kungiyarsa gasar Firimiya ta bana.

Man U ta lallasa QPR da ta hau ajin Firimiya a bana, da ci 4 da 1 a Old Trafford ranar lahadi, inda kocin dan kasar Holland ya samu nasararsa ta farko tun bayan zuwansa kungiyar.

Van Gaal ya ce yana son lashe gasar Firimiya, ko ba a bana ba, to a shekararsa ta biyu ko ta uku, ya ce yana son bai wa magoya bayan kungiyar tukwicin kofi.

An bai wa sabon kocin wanda ya lashe gasar La liga a shekararsa ta farko da ya je Barcelona da kuma Bundesliga a shekarar da ya Bayern Munich, sharadin ya sanya Man U a cikin kungiyoyi uku na saman tebur a karshen gasar Firimiya ta bana.

Bayan cin wasanni biyu kadai cikin karawa hudu da ta yi a karkashin jagorancin Van Gaal, Man United ta inganta salon taka ledarta sosai a fafatawar da ta yi da QPR.

Sabbin shiga kungiyar Angel Di Maria da Ander Herrera sun ci kwallayensu na farko a kungiyar, yayin da Wayne Rooney da Juan Mata su ma suka jefa nasu kwallayen.