'Yan Madrid ku ba ni lokaci-Rodriguez

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ancelotti ya ce yana jin bana kamar bara sai ya sake salon taka ledar 'yan wasansa

Dan wasa mafi cin kwallo a gasar cin kofin duniya, James Rodriguez ya ce har yanzu yana kokarin sabawa a Real Madrid, yayin da kungiyar ke tunkarar gasar zakarun Turai ranar Talata.

Dan wasan na kasar Colombia, da aka dauke shi daga Monaco a lokacin musayar 'yan wasa a kan kimanin fam miliyan 71, na kokarin taka rawar gani da kungiyar zakarun na Turai.

Rodriguez ya ce "Ina kara gogewa a kullum, ta kowacce fuska." Madrid dai na cikin rukuni daya da Liverpool.

Dan wasan mai shekaru 23, ya buga wa Real Madrid wadda ta yi rashin nasarar wasanni biyu cikin uku da ta buga a gasar La Liga, inda a yanzu kungiyar take a matsayina 12 a kan tebur.

Kwallonsa daya tilo da ya ci, ita ce wadda Madrid ta yi canjaras 1 da 1 da Atletico a gasar Super Cup ta Spaniya, daga bisani kuma aka cinye ta a karawa ta biyu.

Akwai bukatar Carlo Ancelotti ya zartar da shawara a kan ko zai ci gaba da sa Iker Casillas, wanda wasu 'yan kallo suka yi wa ihu ranar asabar lokacin da Madrid ta sha kashi, ko kuma ya fara amfani da sabon golan da kungiyar ta dauka, Keylor Navas.