'Za mu tunkari Razgrad tamkar sa'o'inmu'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodgers ya ce za su karbi abokan karawar nasu kamar yadda za su karrama Madrid

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya ce kungiyarsa za ta tunkari abokan karawarta, Ludogorets Razgrad tamkar tana fafatawa da Zakarar Turai, Real Madrid.

Liverpool wadda ta ci Gasar Zakarun Turai har sau biyar za ta karbi bakuncin Ludogorets yau a Anfield.

Rodgers ya ce Gasar Zakarun Turai ta manyan kungiyoyin wasanni ne, don haka kowa daya yake a idon Liverpool.

Rabon Liverpool da zuwa gasar tun karawar da ta yi da Fiorentina a gida inda ta sha kashi da ci 2 da 1 ranar 9 ga watan Disambar 2009.

Sai dai, ta yi nasarar samun shiga gasar ne, bayan ta kammala gasar Firimiyar bara a matsayina biyu.

An kafa kungiyar Ludogorets wadda filin wasanta ke daukar 'yan kallo dubu shida a shekara ta 2001.

Wannan ne karon farko, da kungiyar ta taba zuwa Gasar Zakarun Turai, bayan an fitar da ita a zagaye na biyu na wasan samun cancanta a bara.