Wani Bafaranshe zai kalubalanci Blatter

Image caption Champagne ya ce akwai bukatar a yi gyara kan rashin daidaiton da ake samu a harkar wasanni a karni na 21

Wani Bafaranshe, Jerome Champagne ya tabbatar da kudurinsa na kalubalantar Sepp Blatter a matsayin shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa.

A cikin makon jiya ne, Sepp Blatter ya bayyana niyyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin Fifa a karo na biyar.

Tsohon jami'in diplomasiyyar, Jerome Champagne, mai shekaru 56, ya yi aiki a matsayin jami'in Fifa tsawon shekaru 11 kafin ya bar aiki a 2010.

Bafaranshen ya wallafa a shafinsa na zumunta cewa "Na rubuta wasika ga kwamitin gudanar da zaben Fifa da shugabansa, Mr Domenico Scala, inda na tabbatar musu da aniyata ta tsaya wa takarar shugaban Hukumar."

Champagne dai na da bukatar samun goyon bayan Hukumomin kwallon kafa guda biyar, ko da yake, ba a neman ya bayyana su har sai a watan Janairu lokacin da zai yi shelar takararsa a hukumance.

Za a gudanar da zaben shugaban Hukumar Fifa ne cikin watan Yunin shekara mai kamawa.