Madrid ta yi ragargaza a Gasar Zakaru

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Gerrard ne ya ci fanaretin da ya bai wa Liverpool nasara a kan abokiyar karawarta

Ga alama kungiyar Real Madrid da ke kare kambunta a Gasar Zakarun Turai bana, ba ta je da wasa ba, inda ta lallasa FC Basel da ci 5 da 1.

Kwallon Karim Benzema a minti na 79 ce ta dinke nasarar Real Madrid.

Dan wasan kungiyar Basel, Suchy ne ya fara cin kansu a minti 14 da take leda, sai kwallayen Gareth Bale, Cristiano Ronaldo da sabon dan wasan kungiyar RodrĂ­guez suka dinga biyo baya.

González ne ya farke wa kungiyarsa Basel kwallo daya tilo da ta ci Madrid.

Sauran wasannin kuma Olympiakos ta lallasa Atletico Madrid da ci 3 da 2, sai Juventus ta ci Malmo FF 2 da nema, Monaco ta ci Bayer Leverkusen kwallo 1 mai ban haushi. Benfica ta sha kunya a gaban magoya bayanta a hannun Zenith da ci 2 da nema. Galatasaray ta farke kwallon da Anderlecht ta fara jefa mata, aka tashi kunnen doki 1-1. Borussia Dortmund ta casa Arsenal da ci 2 da nema