'Hazard ka iya zama hamshakin dan kwallo'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mourinho ya soki Hazard kan rashin azancin tsare gida, lokacin da Atletico ta fitar da Chelsea a Gasar Zakaru.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce dan wasan gaban kungiyar, Eden Hazard ka iya sa hannu kan wata sabuwar kwanturagi cikin watan nan a kudurinsa na zama daya daga cikin gawurtattun 'yan kwallo a zamaninsa.

Dan wasan na kasar Belgium mai shekaru 23, ya shiga Chelsea ne daga Lille a shekara ta 2012, kuma a yanzu yana da sauran shekaru uku a kwanturaginsa.

Mourinho ya ce wannan batu ne kawai na lokaci, cikin wata daya ne ko sama da haka amma dai a karshe za mu amince da sabuwar kwanturagi.

Ya ce dan wasan yana son ya ci gaba da zama don bugawa Chelsea kwallo a shekaru masu zuwa.

Kocin ya bayyana Hazard a matsayin gagarumin dan wasa da ke burin ya bunkasa zuwa daya daga cikin hamshakan 'yan kwallo.

Mourinho ya ce suna da gagarumin fata a kan dan wasan cewa zai bunkasa daga wani fitaccen dan kwallo ya kara samun daukaka.