Gervinho ya kara kwanturaginsa da Roma

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa ran dan wasan zai buga wasansu na farko a Gasar Zakarun Turai, da CSKA Moscow a gobe laraba.

Dan wasan gaban Ivory Coast, Gervinho ya sanya hannu kan kwanturagin tsawaita zama a kungiyar Roma ta Italiya zuwa shekara ta 2018.

Dan wasan mai shekaru 27 ya shiga Roma ne daga Arsenal a 2013, ya kuma ci kwallaye tara a wasanni 33 da ya buga.

Roma ta buga a shafinta na intanet cewa: "Yao Gervais Kouassi (Gervinho) ya tsawaita da kwanturaginsa da shekara daya."

Kungiyar ta kammala gasar Serie A a matsayina biyu bara, inda ta samu gurbi a Gasar Zakarun Turai.

A cikin makon jiya ne, Gervinho ya jefa kwallonsa ta farko a kakar wasannin bana, inda Roma ta cinye Fiorentina 2 da nema.