Raunin 'yan wasa zai cuci Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guardiola ya ce rashin zuwan Man U gasar a bana, wani abun gargadi ne ga manyan kungiyoyi

Kungiyar Bayern Munich da ta ci Gasar Zakarun Turai sau biyar za ta fafata, ba tare da Franck Ribery ba, a lokaci guda kuma ana tantama a kan ko Arjen Robben zai buga karawar tasu da Manchester City.

Tsohon dan wasan Faransar mai shekaru 31, ya dawo daga doguwar jinyar raunin da ya ji a gwiwa ranar Asabar, don haka kocin kungiyar, Pep Guardiola ya ce Ribery ba zai buga ba.

Shi ma Robben da ke fama da matsalar ciwon gwiwa, ka iya rasa damar buga wasan na yau.

Ita ma abokiyar karawar, Man City za ta fito ne, ba tare da dan wasanta na gaba ba, Stevan Jovetic da dan bayanta Pablo Zabaleta.

Bayern Munich na fama da matsalar raunin 'yan wasa, inda dan bayanta Holger Badstuber ya samu cirar nama a cinyarsa ranar Asabar don haka sai an yi masa aiki.

Badstuber ya bi sahun Bastian Schweinsteiger da Thiago Alcantara, Rafinha da kuma Javi Martinez.