Bayern Munich ta doke Man City 1-0

Bayern Beat Man City Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern ta samu maki uku kenan akan Manchester City

Bayern Munich ta lashe Manchester City da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara ranar Laraba a Allianze Arena dake Jamus.

Tsohon dan kwallon City mai tsaron baya Jerome Boateng ne ya zura kwallo a raga daf a tashi wasa daga bugun kwana da Joe Hart ya kasa tare kwallo.

Golan City Hart ya ceci kungiyar a karo da dama lokacin da Thomas Muller da Mario Gotze da kuma Boateng suka kai hare-hare a karo daban-daban.

City ta samu damar farke kwallo ta hannun Sergio Aguero shima daf a tashi wasa, lokacin da ya wuce Dante ya buga kwallo ta yi waje daf da turke.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Roma 5 - 1 CSKA Moscow Ajax 1 - 1 Paris St G Barcelona 1 - 0 Apoel Nic Chelsea 1 - 1 FC Schalke 04 NK Maribor 1 - 1 Sporting Ath Bilbao 0 - 0 Shakt Donsk FC Porto 6 - 0 BATE Bor