Saliyo ta kori kocinta McKinstry

Johnny McKinstry
Image caption Johnny McKinstry ya ce bai ji dadi da aka sallame shi ba

Kasar Saliyo ta kori kocinta Johnny McKinstry bayan da ya jagoranci tawagar 'yan kwallon kasar na tsawon watanni shida.

An kori kocin ne bayan da Saliyo tasha kashi a hannun Ivory Coast da Jamhuriyar Congo a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na badi.

Hakan yasa Saliyo a matsayi na karshe a rukuni na hudu ba tare da maki ko daya ba.

Daraktan wasannin rikon kwarya na Saliyo Saidu Mansaray ya sanar wa da BBC ce wa sun sallami McKinstry daga aiki saboda rashin sakamako mai kyau da ya kasa samu.

Kocin mai shekaru 29 an fara nada shi kocin rikon kwaryar tawagar Saliyo a watan Afirilun bara, bayan da Lars Olof Mattson ya yi ritaya.