CAF ta hana Guinea da Saliyo wasa a gida

CAF Logo Hakkin mallakar hoto
Image caption Sau biyu kenan Saliyo za ta karbi bakunci wasa ba a kasarta ba

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta dakatar da Guinea da kuma Saliyo daga karbar bakuncin wasannin da za su kara a gasar neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a watan gobe.

CAF ta ce a yanzu za a yi karawa tsakanin Guinea da Ghana ne a Morocco ranar 11 ga watan Oktoba a filin wasa na Mohamed V a Casablanca.

Yayin da Saliyo za ta taka leda tsakaninta da Kamaru a filin wasa na Ahmadou Ahidjo a Yaounde, ranar 10 ga watan Oktoba, sannan su sake karawa kwanaki uku tsakani.

Saliyo ta karbi bakuncin Jamhuriyar Congo a Lubumbashi a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai cikin watan Satumba.

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dauki wannan matakin ne domin kaura ce wa kamuwa da cutar Ebola.

Sama da mutane 3,000 ne suka mutu a Guinea da Saliyo da Liberia sakamakon kamuwa da cutar Ebola in ji hukumar lafiya ta duniya da ta fitar.