FIFA: Garcia ya bukaci wallafa bincikensa

FIFA Logo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption FIFA za ta gudanar da taron kwamitin amintattu

Lauyan Amurka Michael Garcia ya bukaci hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, da ta wallafa binciken da ya yi kan zargin cin hanci a karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

FIFA tun farko ta sanar da cewar ba za ta bayyana sakamakon binciken lauyan da ya yi kan hanyoyin zawarcin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018 da shekarar 2022 ga al'umma ba.

Garcia ya ce "Ina da yakinin cewa ya zame wa kwamitin amintattun FIFA wajibi su bada izini a wallafa bincikin zargin cin hancin da rashawa ga al'umma".

A shekarar 2010 ne dai aka bai wa Rasha izinin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarar 2018, sannan a ka bai wa Qatar bakuncin gasar shekarar 2022.

Kwamitin amintattun FIFA zai fara taron kwanaki biyu daga ranar Alhamis, cikin batutuwan da zai tattauna har da rahoton binciken da Garcia ya yi kan zargin cin hanci ga mambobin FIFA.