League Cup: Chelsea ta doke Bolton 2-1

Chelsea Win Bolton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ta kai wasan zagaye na gaba a League Cup

Kulob din Chelsea ya kai wasan zagaye na hudu a gasar League Cup, bayan da ya doke Bolton da ci 2-1 a karawar da suka yi a Stamford Bridge ranar Laraba.

Dan kwallon Faransa mai tsaron baya Kurt Zouma ne ya fara zura wa Bolton kwallon a raga a wasansa na farko da ya fara buga wa Chelsea tamaula a mintuna na 25 da fara tamaula.

Nan danan Bolton ta farke kwallonta ta hannun Matt Mills a kwallon da ya ci da kai, mintuna hudu tsakanin kwallon da aka zura musu a raga.

Chelsea, wadda ta kai hare-hare karo 28, ta samu damar zura kwallo ta biyu ta hannun Oscar a mintuna na 55, kuma hakan yasa ta samu kai wa wasan zagayen gaba.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Burton 0 vs 3 Brighton Chelsea 2 vs 1 Bolton Man City 7 vs 0 Sheff Wed Tottenham 3 vs 1 Nottm Forest West Brom 3 vs 2 Hull