Rodgers ya yabi matasan Liverpool

Liverpool Fenarity
Image caption Karawar da aka zura kwallaye 14-13 a bugun fenariti

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya yaba wa Matasan 'yan wasan kungiyar a yadda suka saka kaimi suka doke Middlesbrough a dukan fenarity a gasar League Cup.

Bayan da suka tashi wasa 2-2 a filin Anfield, Liverpool ta kai wasan gaba bayan da ta lashe bugun fenarity da ci 14-13.

Rodgers ya ce "Yan wasan sun nuna kwarewa yayin da suka dinga buga fenaritin da kwarin gwiwa".

Zura kwallaye 14-13 a bugun fenaritin da suka tashi, ya yi kankankan da wasa tsakanin Dagenham & Redbridge ta doke Leyton Orient a watan Agustan 2011.

Wasanni uku ne ke da tarihin cin fenarity da kwallaye 9-8, tsakanin Arsenal da Rotherham a shekarar 2004, Man City ta doke Stoke a shekarar 1982 da kuma Aston Villa inda ta doke Colchester a shekarar 1979