Bayelsa United ta doke Kano Pillars 2-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Web Site
Image caption Sauran wasanni 10 a kammala gasar Premier Nigeria

Kulob din Bayelsa United ya doke Kano Pillars da ci biyu da nema a gasar cin kofin Premier Nigeria wasannin mako na 28 da suka kara a birnin Benin ranar Laraba.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a filaye daban-daban da ke fadin kasar, Sharks ta garin Fatakwal ta doke Kaduna United da ci 3-0, yayin da Nembe City ta yi rashin nasara a hannun Heartland a garin Owerri da ci biyu da nema.

Kungiyar Warri Wolves ta doke Dolphins da ci 3-1, Crown FC ta samu nasara a kan El-Kanemi Warriors da ci daya mai ban haushi, Gombe United ma doke Nasarawa United ta yi da ci daya da nema, sai karawa tsakanin Abia Warriors da Enugu Rangers suka tashi canjaras.

Har yanzu Kano Pillars tana matsayi na daya a teburi bayan buga wasannin mako na 28 da maki 47, sai Warri Wolves da ta koma mataki na biyu da maki 46, yayin da Akwa United ke matsayi na uku da maki 45.

Ga sakamakon wasannin mako na 28 da aka fafata ranar Laraba:

Abia Warriors 0 vs 0 Enugu Rangers Akwa United 2 vs 0 Giwa FC Bayelsa United 2 vs 0 Kano Pillars Crown FC 1 vs 0 El-Kanemi Warriors Gombe United 1 vs 0 Nasarawa United Heartland 2 vs 0 Nembe City FC Lobi Stars 1 vs 0 Enyimba FC Sharks 3 vs 0 Kaduna United Taraba FC 2 vs 2 Sunshine Stars Warri Wolves 3 vs 1 Dolphin