Rodgers ya ce Liverpool ta samu tawaya

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin ya ce raunin Sturridge shima ya kawo musu cikas

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce kulob din ya samu 'yar tawaya, bayan da aka doke su wasanni uku daga cikin wasanni biyar da suka buga a Premier bana.

Rodgers, wanda kulob dinsa ya ke mataki na 11 a teburin Premier, ya ce kawo sababbin 'yan kwallo zuwa kungiyar na daga cikin dalilan da yasa su ke samun tsaiko a gasar.

Ya kara da cewa "Na kirkiro salon da za mu dinga lashe wasanni kamar yadda muka yi watanni 18 baya, abinda ya rage 'yan wasa su kware da salon wasan".

Liverpool ta doke Tottenham 3-0 a White Hart Lane ranar 31 ga watan Agusta, tun daga lokacin ta yi rashin nasara a wasanni biyu da Aston Villa da West Ham suka doke ta.

Liverpool ta kare Premier bara a matsayi na biyu da maki biyu tsakaninta da zakarar kofin Manchester City, sai dai ta sayar da Luis Suarez a bara ta dauko 'yan kwallo tara.