Allardyce na tsoron karo da Man United

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Allardyce ya ce United za ta nemi hucewa a kansa

Kocin West Ham Sam Allardyce ya ce yana tsoron karawar da za su yi da Manchester United a gasar Premier ta Ingila a filin wasa na Old Trafford.

United karkashin koci Louis van Gaal ta yi rashin nasara a wasanni biyu daga cikin wasanni biyar da ta buga Premier bana, ciki har da doke ta 5-3 da Leicester ta yi ranar Lahadi.

Allardyce ya ce "United za ta kara da mu kwanta da kwarkwata irin salon data buga da QPR domin ta ga ta doke mu".

West Ham wadda take a matsayi na takwas a teburin Premier ta doke Liverpool da ci 3-1 a karshen makon da ya wuce.

Cikin wasanni 11 da suka kara a baya, West Ham bata doke United ba, a kakar bara ma United ce ta doke su 3-1 a Old trafford.

Allardyce ya ce ya san rawar da 'yan wasa kamar su Rooney da Radamel Falcao da Angel Di Maria za su taka a karawar ta ranar Asabar.