An yi wa Odemwingie tiyata a kafarsa

Peter Odemwingie Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce zai kara kwazo idan ya murmure

Dan kwallon Stoke City Peter Odemwingie, na fatan murmure wa cikin gaggawa domin ya dawo buga tamaula, bayan tiyatar da likitoci suka yi masa ranar Talata.

Dan wasan Nigeria, mai shekaru 33, ya ji rauni ne a karawar da Stoke ta doke Manchester City a karshen watan Agusta.

Odemwingie ya ce "Ina son murmurewa da wuri, domin na ci gaba da kwazo na daga lokacin dana ji rauni don ciyar da kulob dina gaba".

Dan wasan yana son ya buga wa Nigeria gasar cin kofin Nahiyar Afirka a badi, idan kasar ta samu tikitin zuwa gasar.

Tsohon dan kwallon West Brom din ya zura kwallaye biyar a wasanni 15 da ya buga wa Stoke City, bayan ya koma kulob din daga kungiyar Cardiff a watan Janairu.