Man U na fargabar wasanta na Asabar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal ya ce akwai banbanci tsakanin wasan matasa da na Firtimiya amma dai gwani yana iya fito da kansa

Kocin Manchester United, Louis Van Gaal ya ce babban dan baya daya ne kadai ya rage wa kungiyar don karawar Firimiya da za ta yi da West Ham ranar Asabar.

Kocin ya ce Marcos Rojo ne kadai yake da koshin lafiya, amma Chris Smalling na fama da kafa, Phil Jones kuma gwiwa, raunin idon sawu na damun Evans, an kuma dakatar da Tyler Blackett.

Ya ce duk 'yan wasansa na dama a baya ba sa nan, don haka sai dai ya yi amfani da matasan 'yan kwallo.

'Yan wasan da ake gani Man U za ta yi amfani da su a wasan na gobe, sun hadar da Tom Thorpe mai shekaru 21 da Paddy McNair dan shekara 19.

Haka zalika, ana sa ran Luke Shaw zai yi wasansa na farko a kulob din bayan kammala sayensa a ka fam miliyan 28 daga Southampton, yayin da ake tsammanin Rojo zai matsa gaba a karawarsu ta gobe.

Van Gaal ya ce "Ba na kasada da 'yan wasa-sai suna da koshin lafiya zan saka su wasa"