Rooney ba zai buga wasanni uku ba

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wannan shine karo na uku da Rooney ke samun jan kati a zamansa a Manchester United

Dan wasan gaban Manchester United Wayne Rooney, ba zai buga wasannin uku masu zuwa ba a gasar Premier ta Ingila, bayan jan kati da alkali ya bashi a wasansu da West Ham.

An baiwa Rooney katin ne bayan da ya yiwa dan wasan West Ham Stewart Downing shigar mugunta.

Man U ta samu nasara da ci 2-1 a wasan, sai dai katin da aka baiwa dan wasan ya dishe hasken wasan, inda magoya bayan kungiyar suka nuna bacin ransu.

Wannan jan kati da alkalin wasan ya baiwa Rooney na nufin dan wasan ba zai buga wasanninsu da tsohuwar kungiyarsa ta Everton da West Brom da kuma Chelsea da za su kara a nan gaba.

Wannan shine karo na uku da Rooney mai shekaru 28 ya samu jan kati a zamansa a kungiyar ta Man U.