Ramsy da Arteta za su yi jinya

Aaron Ramsey Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan ba za su buga wa Arsenal wasanni biyu ba

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce Aaron Ramsey da Mikel Arteta za su yi jinyar raunuka da ba za su buga wasa da Galatasaray da Chelsea ba.

An sauya 'yan wasan biyu a karawar da suka tashi 1-1 a wasan hamayya da Tottenham ranar Asabar.

Arsenal za ta fafata da Galatasaray a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Laraba, kafin ta kara da Chelsea kwanaki hudu tsakani a wasan Premier.

Jack Wilshere shi ma sai sauya shi aka yi a karawa da Tottenham a mintuna na 63, wanda babu tabbas ko zai buga wasansu da Galatasaray.

Wenger ya ce ya damu da raunin da 'yan kwallon Arsenal ke ji, ganin Olivier Giroud da Abou Diaby da Mathieu Debuchy da Theo Walcott suna jinya, ga kuma Ramsy da Arteta suma za suyi jinya.